Da rabon shan ruwa gaba: Mata 3 daga cikin 15 da Boko Haram ta sace sun tsere

Da rabon shan ruwa gaba: Mata 3 daga cikin 15 da Boko Haram ta sace sun tsere

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta ke samu daga jaridar RFI Hausa, na nuni da cewa mata uku daga cikin mata 15 da 'yan ta'addan Boko Haram suka sace a yankin Diffa da ke kusa da iyakar Nigeria da Jamhuriyyar Nijar, a ranar 24 ga watan Nuwambar wannan shekarar, sun samu sanarar tserewa, tare da shiga hannun mahukuntan kasar.

Kungiyar Urgence Diffa, wacce ta tabbatar da kubutar matan uku daga hannun Boko Haram, ta kuma tabbatar da cewa a ranar Talata ne ake sa ran mahukuntan yankin na Diffa za su mika matan 3 a hannun iyalansu.

KARANTA WANNAN: Boko Haram yanzu na dauko sojin haya daga mayakan kasashen waje - Tukur Buratai

Da rabon shan ruwa gaba: Mata 3 daga cikin 15 da Boko Haram ta sace sun tsere
Da rabon shan ruwa gaba: Mata 3 daga cikin 15 da Boko Haram ta sace sun tsere
Asali: Twitter

A daren ranar 24 ga watan Nuwamba ne 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram suka kai wani harin ba zata tare da sace 'yan mata 9 a garin Blaharde da kuma wasu 6 a garin Bandé da ke kusa da Toumour.

Haka zalika, Legit.ng ta tattara bayani kan cewa akwai wasu mata da kananan yara sama da 30 da 'yan ta'addan Boko Haram suka sace a garin Ngalewa a jihar Diffa, gabanin sace 'yan matan 9.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel