Dalilin da ya sa nake tare da Atiku Abubakar – Inji Buba Galadima

Dalilin da ya sa nake tare da Atiku Abubakar – Inji Buba Galadima

Mun samu labari daga Jaridar BBC Hausa cewa Injiniya Buba Galadima yana cikin wadanda ke yi wa PDP aiki wajen ganin an tika Shugaba Muhammadu Buhari da kasa a zaben da za ayi a shekarar 2019.

Dalilin da ya sa nake tare da Atiku Abubakar – Inji Buba Galadima
Buba Galadima yana cikin kwamitin yakin neman zaben PDP
Asali: UGC

Buba Galadima wanda ya taba rike Sakatare na tsohouwar Jam’iyyar nan ta CPC mai adawa a 2011 ya bayyana dalilin da ya sa yake tare da Atiku Abubakar na Jam’iyyar hamayya. Galadima yana cikin kwamitin yakin neman zaben Atiku.

Injiniya Buba Galadima dai shi ne ya jagoranci Kungiyar ta-ware na r-APC kafin su narke su shigo cikin tafiyar Jam’iyyar PDP. Galadima ya fadawa BBC Hausa cewa abubuwa sun sukurkuce ainun a Najeriya a mulkin Shugaban kasa Buhari.

KU KARANTA: 2019: Atiku ya dinke barakar sa da Inyamuran Jam’iyyar PDP

Galadima ya kuma ce dole su dage wajen ganin Shugaba Buhari ya sha kashi a zaben badi domin abubuwa su mike a kasar. Injiniyan ya sha alwashin ganin PDP ta lashe zaben na Shugaban kasa da za a yi inda Atiku zai kara da Buhari a PDP.

Tsohon ‘Dan gani-kashe-nin na Buhari ya tabbatar da cewa yanzu yana cikin wadanda su ke aiki a kwamitin yakin neman zaben Atiku domin ganin Buhari ya bar kujerar sa. Galadima yace bai tantamar cewa PDP za ta lashe babban zabe a 2019.

Jiya kun ji cewa ‘Dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana yadda zai bi ya kawo karshen Boko Haram idan har ya samu mulkin kasar nan a zaben da za ayi a shekara mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel