APC da PDP Danjuma ne da Danjummai - Jam'iyyar GNP

APC da PDP Danjuma ne da Danjummai - Jam'iyyar GNP

Mr Santos Larab, wani malamin jami'a kuma dan takarar sanatan mazabar Plateau ta tsakiya karkashin jam'iyyar GNP, ya zargi jam'iyyun APC da PDP ta jefa Najeriya cikin matsalolin da kasar ke fama da su a yanzu.

Laraba ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Litinin a Jos cewa jam'iyyun biyu sun kwashe shekaru masu yawa suna karya alkawurran da suka yiwa 'yan Najeriya.

"Ya zama dole 'yan Najeriya su bai wa sabbin jam'iyyu dama, ya zama dole mu gwada sabbin shugabani idan muna son jagoranci na gari," inji shi.

APC da PDP Danjuma ne da Danjummai - Jam'iyyar GNP
APC da PDP Danjuma ne da Danjummai - Jam'iyyar GNP
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Atiku da Buhari za su iya faduwa zaben 2019 - Faston da ya yi hasashen nasarar Buhari a 2015

Larab ya ce jam'iyyun APC da PDP 'Danjumma ne da Danjummai', ya kara da cewa bayan 'yan Najeriya sun fattatki PDP, sun gano cewa APC ma ake maye gurbinsu da PDP ba su tabbuka wani abin azo a gani ba.

"APC da PDP duk daya ne; jiga-jigan jam'iyyun duk mutane guda ne. Shawara ta ga 'yan Najeriya shine su bawa GPN dama su ga banbanci domin an kafa jam'iyyar ne kan akida mai kyau," inji shi.

A kan takarar zabensa, malamin jami'an ya ce ya shiga takarar ne domin ya bayar da gudunmawarsa wajen inganta rayuwar yan Najeriya.

"Anyi watsi da al'umma ta na lokaci mai tsawo. Bana son a cigaba da tafiya a hakan," inji shi.

Larab ya ce shine ya fi cancanta ya jagorancin al'ummarsa saboda ya dade yana rayuwa cikinsu.

"Roko na ga al'ummar Plateau da na Najeriya shine su zabi GNP a dukkan matakai domin samun shugabanci nagari da yayan mu da jikokinmu za su tashi su mora," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel