Al-Makura ya sallami Basa, Rajistra da shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta Nassarawa

Al-Makura ya sallami Basa, Rajistra da shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta Nassarawa

Gwamnan jahar Nassarawa, Umar Tanko Al-Makura ya sallami shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta jahar Nassarawa dake garin Lafiya, NASPOLY, Dakta Silas Gyar, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.com ta ruwaito shugaban hukumar gudanarwar kwalejin, Mohammed Bako ne ya sanar da haka a ranar Juma’a 30 ga watan Nuwamba, inda yace gwamnati ya dauki matakin ne bayan samun rahoton binciken shugaban kwalejin da aka yi.

KU KARANTA: Mataimakin Atiku Abubakar ya tabbatar da babu hannun Buhari a cikin matsalolin najeriya

Haka zalika Gwamna Al-Makura ya sallami harda rajistran makarantar, Labani Joseph-Dio da kuma jami’in kula da kudi na makarantar, Abdullahi Akyo, inda Mohammed yace sallamar ta fara ne nan take.

Gwamnatin jahar ta kafa kwamitin bincike akan shugaban kwalejin, Silas Gyar, rajistran makarantar, Labani Joseph-Dio da kuma jami’in kula da kudi na makarantar, Abdullahi Akyo, bayan samun korafe korafe akansu na cewa sun ci kudin makarantar naira biliyan biyu.

Sai dai bayan kammala bincike, sakamakon binciken ya tabbatar da sun ci kudaden, don haka ya yanke shawarar sallamarsu daga aiki, tare da umartarsu dasu dawo ma gwamnati kudin gaba daya, naira biliyan biyu.

A wani labarin kuma, Gwamna Tanko Al-Makura ya aika da sunayen mutane goma sha daya da yake muradin nadasu mukaman kwamishina a jahar, ga majalisar dokokin jahar Nassarawa don su tantancesu tare da tabbatar da sahihancinsu.

Kaakakin majalisar jahar Nassarawa, Ibrahim Abadullahi ne ya bayyana haka bayan dan majalisa Tanko Tunga ya karanta wasikar da gwamnan ya aike ma majalisar a zaman majalisar na ranar Litinin 27 ga watan Nuwamba.

Bayan kammala karanta wasikar ne sai Kaakakin majalisar ya bukaci dukkancin mutane goma sha dayan da gwamnan ya aika da sunayensu dasu mika ma majalisar takardar bayanai akansu zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba, inda yace majalisar zata fara tantancesu zuwa ranar 3 ga watan Disamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel