An gano yadda matasa ke amfani da audugar jinin haila domin maye

An gano yadda matasa ke amfani da audugar jinin haila domin maye

Mahukunta a kasar Indonesia sunyi gargadi cewa yanzu matasa sun koma dafa audugar jinin haila cikin ruwan zafi sannan daga baya su sha ruwan domin suyi maye.

Jaridu da dama a kasar wanda suka hada da Jakarda Post, Jawa Post da Post Belitung sun wallafa rahotanni da ke gargadi kan bullowar wannan dabi'a mai tayar da hankula.

An gano cewar matasan kasar Indonesia na amfani da sabuwar audugan har ma da wadda akayi amfani da ita domin su bugu ba tare da karya doka ba ta hanyar sayar haramtattun kwayoyi.

An gano yadda matasa ke amfani da audugar jinin haila domin maye
An gano yadda matasa ke amfani da audugar jinin haila domin maye
Asali: Twitter

Sinadaran Chemicals din da ke cikin audugan matan ne ka janyo maye ko buguwa ga masu sha idan an dafa cikin ruwan zafi a cewar hukumar yaki da miyagun kwayoyi na Indonesia (BNN).

DUBA WANNAN: Shari'ar Maryam Sanda: Shedu sun fadawa kotu yadda aka kashe Bilyaminu

Yan sanda a garin Java da ke babban birnin kasar Jakarta sun kama matasa da dama a buge wanda daga bisani suka bayyana cewa sun bugu ne bayan sun sha ruwan da aka daga audugun mata a cikin kamar yadda Straits Times ta ruwaito.

"Ana nemo audugan matan ne daga bola sannan a jefa cikin tafasashen ruwa. Daga bisani idan ya yi sanyi sai a zauna a kwankwada," inji babban kwamanda Suprinarto, shugaban hukumar BNN da ke Central Java.

Wani yaro dan shekaru 14 da aka kama a Belitung da ke gabashin Sumatra ya amsa cewar ya bugu ne bayan shan ruwan audugan matan kuma ya bayyana wa manema labarai yadda ake dafa ruwan mayen.

Ma'aikatan Lafiya na Indonesia tana gudanar da bincike a kan sinadarin chemical din da ke janyo mayen idan an dafa audugan matan cikin ruwan zafi a cewar wani kafan yada labarai na intanet mai suna Vice.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel