An kamo bakwai daga 13 da suka saci ma'aikaciyar lafiya a kwanakin baya

An kamo bakwai daga 13 da suka saci ma'aikaciyar lafiya a kwanakin baya

- An cafke wadanda sukayi garkuwa da wani ma'aikacin lafiya

- Sun nemi a biya N350,000 kafin su sakeshi

- Har yanzu ana cigaba da neman ragowar mutum Biyu

An kamo bakwai daga 13 da suka saci ma'aikaciyar lafiya a kwanakin baya
An kamo bakwai daga 13 da suka saci ma'aikaciyar lafiya a kwanakin baya
Asali: Facebook

Jami'an yan sandan jihar Adamawa sun samu nasarar cafke mutane Biyar masu garkuwa da mutane a Yola.

Mutane Biyar din suna zaune ne a wani kauye mai suna Balma sannan akwai sa hannun su a yin garkuwa da wani ma'aikacin lafiya mai suna Thakma Dabala.

Da ake tattaunawa da Dabala yace ya zauna tsayin kwanaki 15 a hannun mutanen kafin daga bisani wani dan uwanshi ya biya N350,000 sannan suka sake shi.

Yan sandan sun kara da cewa har zuwa yanzu ana cigaba da neman ragowar mutane Biyu.

DUBA WANNAN: Yadda DSS tayi da Oshiomhole kan zargin cin hanci a APC

A Najeriya dai, ran talaka ya zama kamar banza, ana kama mutane ko a kashe ko ayi garkuwa dasu domin neman kudin fansa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel