Marigayi Yar'Adua ne ya yi sanadiyar tsananta ta'addancin Boko Haram a Najeriya - Obasanjo

Marigayi Yar'Adua ne ya yi sanadiyar tsananta ta'addancin Boko Haram a Najeriya - Obasanjo

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya kalubalanci takwaransa, Marigayi Umar Musa Yar' Adua da sanadiyar tsananta ta'addancin kungiyar Boko Haram a Najeriya.

Tsohon shugaban kasa Olusegun ya bayyana hakan ne cikin wani shiri mai taken "The Talk" da aka watsa a tashar You Tube ta "Voice Of the People", watau Muryar Al'umma.

Cikin wannan shiri da Obasanjo ke amsa tambayoyi na bayyana matsayi da mukaman wasu jiga-jigai na kasar nan ya bayyana Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya da kuma Farfesa Yemi Osinbaja a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Sai dai a wannan shiri Obasanjo ya bayyana cewa a halin yanzu ko kadan ba ya da masaniyar wani mukami ko matsayi da tsohon gwamnan jihar Legas ke rike da shi, Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar APC, sai dai ya na da tabbacin kasancewar Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa ta Najeriya.

Marigayi Yar'Adua ne ya tsananta ta'addancin Boko Haram a Najeriya - Obasanjo
Marigayi Yar'Adua ne ya tsananta ta'addancin Boko Haram a Najeriya - Obasanjo
Asali: Instagram

Yayin da tafiya tayi tafiya cikin wannan shiri, Obasanjo ya bayyana cewa rikon sakainar kashi da marigayi tsohon shugaban kasa Yar Adua ya yiwa kungiyar Boko Haram a shekarar 2007 ya yi sanadiyar tsananta ta'addancin a kasar nan.

KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta hori al'ummar Kasa akan gujewa munanan kalamai game da Najeriya

Obasanjo wanda ya yi bugun gaba da cewar da ya kasance shugaban kasa a wannan lokaci da tuni Boko Haram ta zamto tarihi a kasar nan.

Kazalika tsohon shugaban kasar ya soki gwamnatin shugaba Buhari da cewar ba bu abinda ta tsinana kasar nan kuma a matsayinsa na Dattijon kirki zai ci gaba da tsawatar a duk sa'ilin da aka yi ba daidai ba cikin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel