Wasika ta musamman daga babban Editan jaridar Legit.ng (NAIJ.com)

Wasika ta musamman daga babban Editan jaridar Legit.ng (NAIJ.com)

Zuwa ga masu karatu: Sunana Bayo Olupohunda, babban Editan jaridar Legit.ng wacce a baya kuka santa da Naij.com.

Kamar yadda kuka sani, NAIJ.com ta samu babban sauyi zuwa Legit.ng. Bari na yi amfani da wannan damar don sanar da ku manya manyan sauye sauyen da aka samu a tsawon wannan lokaci.

Hakika tawagar ma'aikatanmu a kullum na aiki tukuru don samar da wani sabon al'amari. Tun daga shekara ta 2012 muke samar da bayanai, labarai, hotuna, bidiyo, a fannoni daban daban kuma cikin tsari daban daban, don cimma muradun masu bibiyarmu, da kuma samar da amintaccen bayani na gaskiya.

Ko kadan, bamu taba yin fargaba, ko nuna jin tsoro wajen samar da wani abu sabo wanda zai tafi da salo da tsari na zamani ba. Hakika, wannan ne ma yasa a yanzu, muka bugi kirji, muka kawo babban sauyi - shine 'canjin suna'.

Daya daga cikin babban muradinmu shine 'Martaba'. Muna iya bakin kokarinmu wajen binciko gaskiya kafin mu sanar da jama'a don kauce jefa masu bibiyarmu cikin rudani ko shakku. Wala-Allah wannan ne babban dalilinmu na sauya suna zuwa Legit.ng.

Wannan sabon suna ya fayyace gaskiya ma'anarmu da kuma manufofinmu, hakan kuma zai taimaka ainun wajen baiwa jama'a damar fahimtarmu.

Wasika ta musamman daga babban Editan jaridar Legit.ng (tsohuwar jaridar NAIJ.com)
Wasika ta musamman daga babban Editan jaridar Legit.ng (tsohuwar jaridar NAIJ.com)
Asali: UGC

Hakika muna da kyakkyawar makoma, ta ci gaba da fayyace gaskiya akan dukkanin muhimman abubuwan da suke faruwa a Nigeria. Duk da cewa, a Legit.ng zaka karu da wasu bangarori da dama na rayuwa, kama daga samun nishadi ta hanyar karatu ko kuma nishadantuwa da kayatattun bidiyo ko labaran masana'antar fina-finai da, wake-wake, ado, abinci, al'adu da dai sauransu.

A bangaren samar da hotuna masu motsi da kuma sandararru, wannan mun ciri tuta, kuma muna ci gaba da bunkasa wannan fanni. A yanzu, da muka samu wannan babban sauyin, shafin Legit.ng zai kara zama abokin kowa wajen saukin mu'amala.

Cikin sauki zaka iya lalubar duk bayanin da kake nema; cikin sauki zaka iya bitar muhimman labarai, sanarwa, ko bayanan da kake nema, a ciki ne kuma zaka tsinakayi zafafan al'amura da ke faruwa, labarai da dumi dumi da dai sauransu.

Ina fatan za ku ci gaba da nishadantuwa da wannan sabon canji da muka yi. Na gode da kuka kasance tare damu na tsawon lokaci har zuwa kawo yau da muka sauya suna daga NAIJ.com zuwa Legit.ng.

Ina da yakinin cewa, wannan shine mafarar tafiyar nasararmu a tare.

Bayo Olupohunda

Babban Editan Legit.ng (Naij.com)

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel