Jirgin yaki ya lalata sansanin horar da yan Boko Haram a Malkonory, Borno

Jirgin yaki ya lalata sansanin horar da yan Boko Haram a Malkonory, Borno

- Jirgin yaki na sojin saman Najeriya ya lalata wani sansanin horar da ýan Boko Haram a Malkonory

- Hakazalika sun lalata mutor yan ta’addan a kusa Tumbun Rego a yankin arewacin Borno

- Lamarin ya afku ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba

Rundunar sojin saman Najeriya tace jirginta na Operation Lafiya Dole ta lalata wani sansanin horar da ýan Boko Haram a Malkonory, sannan kuma sun lalata mutor yan ta’addan a kusa Tumbun Rego a yankin arewacin Borno.

Air Commodore Ibikunle Daramola, jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin saman wanda ya bayyana hakan a wani jawabi a Abuja a ranar Alhamis, yace an gudanar da aikin ne a ranar 11 ga watan Oktoba.

Jirgin yaki ya lalata sansanin horar da yan Boko Haram a Malkonory, Borno

Jirgin yaki ya lalata sansanin horar da yan Boko Haram a Malkonory, Borno
Source: Twitter

Daramola ya bayyana cewa sashin kwararru na NAF wato Intelligence, Surveillance and Reconnaissance (ISR) sun tabbatar da cewa a sansanin akwai maza da dama da ake horarwa.

KU KARANTA KUMA: 2019: Wata kungiya ta bukaci Atiku da ya zabi Fayose a matsayin abokin takara

Kakakin NAF din ya kuma bayyana cewa an halaka sauran tsirarun yan ta’addan a hare-haren da suka biyo baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel