A karo na farko bayan tsige shi, Lawal Daura ya yi magana kan mamaye majalisa

A karo na farko bayan tsige shi, Lawal Daura ya yi magana kan mamaye majalisa

- Tsohon shugaban DSS, Lawal Daura ya ce ya dauki matakin mamaye majalisa ne saboda ya samu bayanan sirri na cewa za'a shigo da muggan makamai cikin majalisa

- Daura ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake alakanta shi da yiwa masu adawa da gwamnati aiki

- Lawal Daura ya ce ba zai bayyana sunan wanda ya bashi izinin mamaye harabar majalisar dattawar ba

Rahoton da muka samu daga Daily Nigerian na cewa tsohon shugaban hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS), Lawal Daura ya ce tun da ya fara aiki babu wata korafi ko kuka da akayi kan yadda yake gudanar da aikinsa amma kwatsam sai gashi an kore shi.

A karo na farko bayan tsige shi, Lawal Daura ya yi magana kan mamaye majalisa
A karo na farko bayan tsige shi, Lawal Daura ya yi magana kan mamaye majalisa
Asali: Depositphotos

Wani na kuda da tsohon shugaban DSS da baya son a fadi sunansa yace Daura yace ya dauki matakin da mamaye majalisar ne saboda ya kare mutuncin kasa duk da ya yi alkawarin ba zai fadi sunan wanda ya bashi umurnin mamaye majalisar ba.

DUBA WANNAN: Kotu tayi fatali da bukatar dakatar da tsige Saraki

Majiyar ta cigaba da cewa "duk da cewa har yanzu Daura bai kammala mika mulki ga wanda zai maye gurbinsa ba a aikace, anyi bincike a gidansa da ke Asokoro da Gwarimpa amma ba'a samu wani haramtaccen abu ba sai dai kayayakin amfani na yau da kulum kuma an mayar masa kayansa."

Majiyar ta kuma ce a lokacin da mukadashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya gayyace Daura, ya tafi cikin hanzari amma kwatsam sai aka fada masa an sallame shi ba tare da ya san laifin da ya aikata ba wanda hakan ya karya lagwansa.

"Daura bai ji dadin yadda ake ta yada sunansa a matsayin wanda ya ke yiwa 'yan adawa aiki duk da cewa ya aikata abinda ya yi ne domin ya kare fadar shugaban kasa amma a yanzu an juya labarin ana cewa shi dan leken asiri ne." A cewar majiyar.

Wannan sabon bayanin ya ci karo da rahoton da Sufeta Janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris ya bayar inda ya ce Daura ya amsa cewa ya tura jami'an DSS ne su mamaye majalisar saboda ya samu rahoton cewa wasu na niyyar shigar da muggan makamai cikin majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel