Rashin kudin magani ya sanya wani kashe dan uwansa mara lafiya don kowa ya huta

Rashin kudin magani ya sanya wani kashe dan uwansa mara lafiya don kowa ya huta

- Kasa jure siyan magani akai-akai saboda tsananin talauci ya sanya wani karasa dan uwansa zuwa lahira

- Sai dai tunu jami'an 'ya sanda suka cafke shi, har yayi jawabi

Wani mutum mai shekaru 40 a duniya ya sheka dan uwansa zuwa barzahu saboda gajiya da biyan kudin magani.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Ugwuagbo dake karamar hukumar Igbo-Eze ta arewa jihar Enugu.

Kaico: Rashin kudin da zai sayawa dan uwansa magani ya sanya shi yanke hukunci kashe sa kowa ya huta
Kaico: Rashin kudin da zai sayawa dan uwansa magani ya sanya shi yanke hukunci kashe sa kowa ya huta

Yanzu haka dai kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar Ebere Amaraizu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce "Mun samu bayanai cewa Raphael Izuchukwu wanda shekarunsa na haihuwa sun kai 40, ya kashe dan uwansa Chizoba Ogbonna mai shekaru 46, sannan ya binne shi a ranar".

KU KARANTA: Uba da 'Da sun yi taron dangin keta haddin wata Budurwa 'Yar shekara 13 a jihar Benuwe

"Yanzu haka dai jami'anmu suna cigaba da fadada bincike kuma mai laifin yana hannu domin cigaba da amsa tambayoyi. Mai laifin dai ya amsa da bakinsa cewa shi ne ya kashe dan uwan nasa sannan ya binne gawarsa a ranar".

Kakakin ‘yan sandan ya cigaba da bayyana cewa "Da muka tuhume sa koma mene ne dalilin kashe dan uwan nasa, sai ya kada baki yace dan uwan nasa ya dade yana rashin lafiya kuma shi ne wanda yake kula da komai nasa, gashi bashi da karfin cigaba da kula da jinyar tasa, hakan tasa ya yanke hukunci kashe shi don kowa ya huta".

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng