Za'a dai-dai ta rabon gado tsakanin maza da mata
Shugaban kasar Tunusiya zai fito da wata sabuwar doka wacce zata daidaita rabon gado tsakanin maza da mata
Shugaban kasar Tunusiya zai fito da wata sabuwar doka wacce zata daidaita rabon gado tsakanin maza da mata.
Shugaban kasar Beji Caid Essebsi ya bayyana cewar zai gabatar da kudurin dokar ne ga majalisar dokokin kasar domin sanya hannu.
DUBA WANNAN: Kuji maganar da Shehu Sani yayi akan rikicin sojoji da aka yi a garin Maiduguri
A tsarin addinin musulunci maza sun fi mata samun kaso mai yawa idan aka zo ta fannin rabon gado, sai dai shi kuma shugaba Essebsi ya bayyana cewa kasar Tunusiya, kasa ce mai sassaucin ra'ayi.
Ana sa ran shugaban kasar zai gabatar da kudurin dai dai ta rabon gadon tsakanin maza da mata a ranar mata ta duniya.
Bayan haka kuma ana ganin shugaban kasar zai gabatar da kudurin kare hakkin 'yan luwadi da madugo, sai dai har ya zuwa yanzu ya ce zai kafa wani kwamiti da zai yo nazari akan kudurin nasa kafin ya bayyana shi domin gujewa fushin al'ummar kasar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng