Yadda wata Muguwar Uwa ta azabtar da karamar yarinya da Reza da Wuta

Yadda wata Muguwar Uwa ta azabtar da karamar yarinya da Reza da Wuta

Wata yar karamar yarinya Khadija mai shekaru 8 ta shiga uku bayan da uwarta, kanwar mahaifinta ta yayyanka mata jiki da reza, yayin da Mijinta ya babbaka duwawun yarinyar da wuta, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Matar mai suna Peace Afolabi ta dauko Khadijat ne daga kauyensu dake jihar Kogi, inda ta kawota gidansu dake jihar Kaduna domin ta rike ta, inda har ta sanya Khadija tana zama a shagonta.

KU KARANTA: Mayakan rundunar Sojan kasa sun yi bore, sun kulle filin sauka da tashin jirage na Maiduguri

Wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Talatar da ta gabata, inda Peace tace Khadija ta sace mata kudi Naira Ashirin (N20), kuma ta sayar mata da kayan shago na naira dari uku (N300) akan bashi.

Wannan ne dalilin da ya sanya a ranar Talatar, Peace ta shiga jibgar Khadiya kamar Allah ya aikota, sa’annan ta sanya reza ta yayyanka mata hannayenta da jikinta, daga bisani kuma Mijinya ya banka ma yarinyar wuta a duwawu.

Majiyarmu ta ruwaito makwabtan ma’auratan suna fadin cewa sun dade suna cutar da Khadija, cin zali, cin zarafi, da kuma horoda yunwa, ga tarin ayyuka da suke sanya ta daban daban kamar wata jaka.

Da aka tuntubi kwamishiniyar al’amuran Mata da cigaban zamantakewa, Hajiya Hafsat Baba, tace ma’aikatarta ta samu nasarar ceto Khadija, inda ta aka garzaya da ita zuwa Asibiti, yayin da aka kama Babartata da Mijinta.

Daga karshe Hajiya Hafsat ta gargadi iyaye da marika da su guji cutar da kananan yara, inda tace duk wanda aka kama da wannan laifi, toh ya yi kuka da kansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel