Irin su Makarfi ake nema su zama Shugaban kasa inji Janar Ibrahim Babangida
Mun samu labari daga Daily Trust cewa Tsohon Shugaban Kasar Najeriya a lokacin mukin Soji, Ibrahim Badamasi Babangida ya yabi daya daga cikin masu neman takarar Shugaban kasa a PDP.
Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana cewa tsohon Gwamna Kaduna Sanata Ahmad Muhammad Makarfi yana cikin irin ‘Yan takarar da ya kamata su mulki kasar nan. IBB yace irin su Makarfi za su iya gyara Najeriya.
KU KARANTA: Zan warewa harkar ilmi kashi 21% cikin kasafin kudi idan na zama Shugaban kasa - Atiku
Tsohon Shugaban kasar a lokacin Soji yace da har ya fara cire ran sa game da gyara Najeriya, sai dai bayan Janar Babangida ya ji jawabin Ahmad Muhammad Makarfi, ya ji akwai alamun nasara idan har irin su na siyasa a Kasar.
Ibrahim Babangida yace dole abubuwa su canza a Najeriya kuma irin su Makarfi ne za su yi wannan aiki. Babangida ya kuma jinjinawa aikin da Ahmad Makarfi yayi lokacin yana Majalisa da kuma yadda ya mulki Jihar Kaduna.
Ahmed Makarfi wanda ya taka har gidan Babangida a Garin Minna domin ya samu tabarruki yana cikin masu neman takara a a 2019. Kwanakin baya dai Ahmad Makarfi yayi magana game da wadanda su ka dawo PDP cikin kwanan nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng