Yansanda sun yi musayar wuta da yan bindiga a Talatar mafara, sun kama 12

Yansanda sun yi musayar wuta da yan bindiga a Talatar mafara, sun kama 12

Rundunar Yansandan jihar Zamfara ya bayyana cewa jami’anta sun yi batakashi da wani gungun yan bindiga da suka yi ma kasuwar dabbobi dake garin Talatar mafara tsinke, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin Yansandan jihar, SP Muhammad Shehu ya bayyana cewa Yansanda sun samu nasara a yayin wannan musayar wuta da aka yi, har ma suka kwato mutane 9 da yan bindigar suka yi garkuwa dasu.

KU KARANTA: Shehu Sani a neman kariyar Allah daga sharrin masharranta da hassadan mahassada

Shehu yace wannan arangama ya faru ne a ranar Talata 31 ga watan Yuli da misalin karfe hudu na rana, inda yan bindigar suka yi kokarin satar shanu tare da karkashe mutane, kamar yadda ya fada a garin Gusau.

“Yan bindigan sun kama mutane Tara, kafin nan suka kokarin shiga kasuwar dabboi na Talatar mafara, sai dai ba tare da wata wata ba Yansandanmu suka mayar da biki, inda aka yi ta musayar wuta har sai da yan bindigan suka ranta ana kare, sa’annan suka ceto mutanen su Tara.” Inji Shehu.

Kaakakin yace sun kama mutum goma sha biyu daga cikin maharan, tare da kwato muggan makamai da kuma kayan tsafe tsafe, sa’annan yace zasu gurfanar dasu gaban Kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Daga karshe Shehu ya shawarci jama’a dasu basu hadin kai da goyon baya, tare da sauran hukumomin tsaro ta hanyar basu ingantattun bayanai game da ayyukan yan ta’addan, don kawar dasu gaba daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng