Yaki ba ayin ka da raggo: Buratai ya nada sabon kwamandan rundunar Lafiya Dole

Yaki ba ayin ka da raggo: Buratai ya nada sabon kwamandan rundunar Lafiya Dole

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya nada Manjo Janar AM Dikko a matsayin sabon kwamandan rundunar yaki da kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram ta Lafiya Dole.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sabuwar sanarwar da mai magana da yawun rundunar sojin kasan Texas Chukwu ya fitar dauke da sa hannun sa a garin Abuja.

Yaki ba ayin ka da raggo: Buratai ya nada sabon kwamandan rundunar Lafiya Dole

Yaki ba ayin ka da raggo: Buratai ya nada sabon kwamandan rundunar Lafiya Dole

KU KARANTA: Jerin yadda girma da mukaman gidan soja suke

Legit.ng ta samu cewa wannan sabon nadin dai zai soma aiki ne daga ranar 1 ga watan Agustan wannan shekarar kuma zai karbi ragamar rundunar ne daga hannun Rogers Nicholas.

A wani labarin kuma, Dakarun sojojin saman Najeriya watau Nigerian Air Force (NAF) ta ce rundunar ta ta shirin ko ta kwana ta musamman dake a karkashin babbar rundunar Operation Lafiya Dole sun yi nasarar yin raga-raga da 'yan ta'addan Boko Haram a kauyukan Bulagalaye da kuma Kwakwa, dukan su a jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar, AVM Olatokunbo Adesanya shine ya sanarwa da manema labarai hakan a ranar Juma'ar da ta gabata a garin Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel