Wani Hadimin Buhari yace Kwankwaso bai yi wa al'ummar Kano aikin komai ba a Majalisa

Wani Hadimin Buhari yace Kwankwaso bai yi wa al'ummar Kano aikin komai ba a Majalisa

Idan ba ku manta ba kwanan nan ne Ministan sufuri na Gwamnatin Buhari watau Rotimi Amaechi ya bayyana cewa Shugaban kasa Buhari ne zai lashe zaben 2019 har a Jihar Kano. Sanata Rabiu Kwankwaso bai bar maganar ta wuce haka ba.

Wani Hadimin Buhari yace Kwankwaso bai yi wa al'ummar Kano aikin komai ba a Majalisa
Mai ba Buhari shawara daga Kano yace Kwankwaso ba zai kai labari ba

Tsohon Gwamnan ya maidawa Ministan martani inda yace babu yadda za ayi Buhari yayi nasara a Kano. Hakan ya sa daya daga cikin masu ba Shugaban kasa shawara a kan kafofin sada zumunta na zamani watau Bashir Ahmad yace da sake.

Bashir Ahmad ya nuna cewa Sanatan na Kano ta tsakiya bai dauki mutanen sa komai ba ganin yadda yayi watsi da su tun da ya tafi Majalisa. Bashir yace babu wani aikin a-zo-a-gani da Kwankwaso yayi a Kano tun da ya zama Sanata har yanzu.

KU KARANTA: Tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso sun hadu da Ibrahim Shekarau

Hadimin Shugaban kasar ta shafin sa na Tuwita yake cewa fiye da shekaru 2 kenan Kwankwaso bai kawo ziyara Jihar Kano ba. Sai dai wasu mutanen sun koka da cewa Shugaba Buhari ma dai yayi watsi da Kano duk kokarin da su kayi a 2015.

Ku na da labari cewa ana tunani tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya bar Jam’iyyar APC kwanan nan zai yi takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP kuma zai iya kawowa Shugaba Muhammadu Buhari cikas a 2019.

Rotimi Amaechi wanda Minista ne a Gwamnatin nan ya bayyana cewa babu abin da zai hana Shugaba Buhari yin nasara a Kano duk da sauya shekan da manyan ‘Yan Majalisar su kayi. Kwankwaso dai bai yarda da hakan ba inda yace sai an buga.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel