Harin Boko Haram a Jakana: Jami'an tsaro sun samu nasarar fitittkansu – Hukumar yan sanda
Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana nasarar da ta samu wajen dakile harin da yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram suka kai garin Jakana, karamar hukumar Konduga a jihar Borno ranan Alhamis da dare.
Kakakin hukumar na jiha, Edet Okon, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a wata jawabin da ya baiwa tashar Channels Talabijin.
Duk da cewa bai bayyana yawan mutanen da aka rasa ba, Okon ya yi bayanin cewa yan Boko Haram din sun shigo garin ne cikin akalla motoci talatin da yammacin Alhamis.
Yace da wuri an tura jami’an yan sandan Special Anti-Robbery Squad (SARS) cikin garin domin taimakawa sojin da kasa.
Suna isa wajen suka tarar rundunar sojin Operation lafiya dole suna musayar wuta da yan ta’addan.
Sai aka kwashe sa’o’I biyu ana musayar wuta kafin aka samu nasarar fitittikan yan Boko Haram daga cikin garin.
Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa yan Boko Haram sun kai mumunan hari Jakana kusa da garin Maiduguri da daren yau Alhamis misalin karfe 9:20.
Jakana wani gari ne da ke hanyar Kano zuwa Maiduguri. Yan Boko Haram basu taba samun nasaran kwace garin duk da hare-haren da yan ta'addan ke kaiwa.
Wata majiya ta bayyanawa jaridar Premium Times cewa maharan sun zo ne da manyan makamai sun kwashe awa daya suna ruwan wuta.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng