EFCC ta cafko Janar na bogi, mai wuru-wuru kan dukiyar mutane

EFCC ta cafko Janar na bogi, mai wuru-wuru kan dukiyar mutane

- Asirin wani dan damfara, dake karyar cewa shi Janar din sojin Najeriya ne ta tonu a jihar Rivers

- An kama dan damfarar, Adesola Bucknor ne bayan ya yi kokarin damfarar shugaban jami'an jihar Rivers, Farfesa Blessinf Diba

- Ya aike wa shugaban jami'ar wasikar naddin mukami a matsayin uwar kungiyar mabiya addinin kirista na Sojin Najeriya kuma ya bukaci ta bayar da wasu kudade don shirya bikin nadinta

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'anati a Nigeria wato EFCC tace jami'anta dake Fatakwal sun damke wani mutum dake yiwa Brig. Janar Dawuk Danfulani na 6 Division Garrison sojin gona a jihar Rivers.

EFCC ta cafko Janar na bogi, mai wuru-wuru kan dukiyar mutane

EFCC ta cafko Janar na bogi, mai wuru-wuru kan dukiyar mutane

Jami'in hulda da jama'a na EFCC, Wilson Uwujaren yace wanda ake tuhumar, Adesola Bucknor, ya nada shugaban jami'ar jihar Rivers, Farfesa Blessing Diba, a matsayin uwar kungiyan Fastocin sojin Najeriya a wata wasika dake dauke sa sunnan Brig. Janar Danfulani.

KU KARANTA: Dan takarar gwamna a PDP ya yi korafin cigaba da tsare shi ga IG

Uwujaren yace a karshen wasikar, Bucknor ya nemi taimakon kudi daga shuganban jami'ar don gudanar da bikin mika godiya ga ubangiji da za'ayi bayan an kammala nadin mukamin da za'ayi mata.

"Saboda ya gamsar da masu karanta wasika naddin, Bucknor ya kirkiro tambarin sashin addinin Kirista na Sojin Najeriya kuma ya kwakwayi sa hannun Janar Danfulani," inji Uwajeren.

Yace bayan anyi bincike a gidan wanda ake tuhumar a garin Fatakwal, an gano wasu takardun bogi da yawa da ke nuna shine ya aikata laifin inda ya kara da cewa cikin kankanin lokaci za'a gurfanar dashi a kotu domin ya fuskanci shari'a.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku labarin yadda 'yan ta'adan Boko Haram suka kai wata mummunan hari a kauyen Jakana dake jihar Borno.

Wannan ya biyo bayan nasarar halaka wasu 'yan ta'adan da dama da sojojin saman Najeriya su kayi cikin farkon makon a yankin na arewa maso gabasin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel