Abin ban tausayi: Yadda wutan lantarki ya yi wata mata da yaranta uku lahani

Abin ban tausayi: Yadda wutan lantarki ya yi wata mata da yaranta uku lahani

Mutanen dake zaune a Dada Olowu street dake Abule Egba a Legas sun fada cikin jimami da bakin ciki sakamakon fadowar babban wayar wutan lantarki a kan shagon wata mata inda wutar ya yi sanadiyar kashe yaro daya da jikkata mutum uku.

Punch Metro ta ruwaito cewa matar mai suna Particia Ossai tana cikin shagon ta ne yayin da wayar da fizge daga jikin pole wire ta fado kan shagon.

Lamarin ya afku ne a ranar Juma'a misalin karfe 11.30 na safiya yayin da ake ruwan sama tare da iska.

Abin tan tausayi: Yadda wutan lantarki ya yi sanadiyar rasuwar wata mata da jinjiirinta
Abin tan tausayi: Yadda wutan lantarki ya yi sanadiyar rasuwar wata mata da jinjiirinta

Majiyar Legit.ng ta gano cewa Patricia da yaranta guda uku sun fadi a sumamu kuma an garzayar dasu zuwa wani asbiti dake kusa da gidansu.

DUBA WANNAN: R-APC zata iya tsayar da dan takarar shugaban kasa - Buba Galadima

Bayan an kai su asibitin ne daya daga cikin yaran mai suna Chidi Ossai ya rasu.

Mijin Partricia, Sunday Ossai, ya shaida wa majiyar Legit.ng cewa yana wajen aiki ne lokacin da aka kira shi a waya aka sanar dashi abinda ya faru.

Yace, "Na kama hayar shagon ne watanni biyu da suka wuce saboda mata na ta samu abin yi. Ina wajen aiki ne sai wani ya kira ni yace mata na da yara suna asibiti.

"Lokacin da na isa asibitin, an umurci ne da biyan kudin kati na mutum uku kuma in biya N100,000 kudin magani kafin in gansu. Daga baya aka fada min yaro na daya ya rasu.

"Na basu N50,000 saboda su fara yiwa wanda suke da rai magani."

Mai gidan hayar da shagon matan yake ya shaidawa manema labarai cewa ma'aikatan kamfanin wutan lantarkin na Ikeja sun zo sun dauke wayar wutan data fado, sun kuma fada masa cewa zasu biya kudaden maganin jinyar matar da yaranta.

Sai dai shigaban sashin hulda da jama'a na Ikeja Electric, Felix Ofulue, bai amsa wayarsa ba kuma bai amsa sakon tes da aka aika masa game da batun ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164