Idan ba ka shan Zoborodo, za ka fara bayan karanta wannan
Zobo wani shahrarren abin sha ne a nahiyar Afrika musamman a Najeriya. Ana kiran ganyen “hibiscus’ da yaren Turanci kuma Zoborod da Hausa.
Karanta jerin sinadaran gina jikin da Zobo ya kunsa:
Vitamin C
Calcium
Iron
Phosphorous
Niacin
Riboflavin
Fibre
Fat
Thiamine
Carotene
Amfanonin sha Zobo takwas:
1. Ya na hana hawan jinni
Bushasshen gayen Zobo na da sinadarin hana hawan jinni da kuma rage yawan Cholsetrol
2. Yana hana ciwon daji
Zobo na da sinadarin Vitamin C da ke da ‘Anthocyanins’ da yawa saboda haka yakan yaki cikin daji
3. Yana hana ciwon siga
Zobo na lura da yawan siga a cikin jinin jiki dan Adam ta hanyar nike abincin da ya kunshi siga
4. Yana kare kodar mutum
Zobo kan hana taruwan uric acid da oxalic acids a kodar mutum. Kana ya kan rage karfin uric acids, citrate, calcium, creatinine, tartrate, sodium, potassium da phosphate a fitasrin dan Adam.
KU KARANTA: Dattijan Arewa sun fiye son kansu, kunya ce ta ishe su suke so su tade kafar Buhari - Fadar shugaban kasa
5. Ya na kara yawan jinni
Yadda ka ganshi da kala ja, haka yake kara yawan jinin dan Adam ta hanyar kara yawan red blood cells da haemoglobin.
6. Ya na taimakawa wajen maganin sanyi
7. Ya na kara karfin kashi ciki
Zobo na da yawan sinadarin Calcium wanda ke kara karfin kasha da kuma kawar da cutan kasha irinsu osteoporosis.
8. Yana kara karfin ido
Kasancewan yana da sinadarin Vitamin A, yana taimakawa gani da kuma hana sauran tsufan ido.
Madogara :healthable.org
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng