Son kowa kin wanda ya rasa: Ronaldo ya sa gidan sa da ke Sifen a kasuwa

Son kowa kin wanda ya rasa: Ronaldo ya sa gidan sa da ke Sifen a kasuwa

- Cristiano Ronaldo na neman mai sayen wani makeken gidan sa

- ‘Dan wasan ya bar Sifen bayan ya koma Kungiuyar Juventus

- Wannan katafaren gida zai kai Euro fam Miliyan 4.8 a kasuwa

Mun samu labari cewa tsohon ‘Dan wasan gaban Real Madrid Cristiano Ronaldo ya sa gidan sa na Garin Madrid da ke Kasar Sifen a kasuwa bayan ya tattara ya bar Kungiyar kwanan nan.

Tsohon ‘Dan wasan na Madrid Cristiano Ronaldo ya koma Kungiyar Juventus da taka leda don haka yake neman wanda zai saye gidan sa a kan kudi kusan Euro fam Miliyan £5. A takaice dai gidan ya kai kusan Naira Biliyan 2.

KU KARANTA: Wani Kulob din Larabawa zai bada Biliyoyin kudi ya saye Ahmed Musa

Babban ‘Dan wasan na Kasar Portugal ya tashi daga Real Madrid ne bayan ya dauki shekaru kusan 9 a Kulob din. Ronaldo ya koma Kasar Italiya bayan da aka saye sa kan kudi Euro fam miliyan £99 a karshen Gasar nan ta bana.

Wannan gida da yake wajen Sifen dai sai wane-da-wane kadai za su iya sayen sa. A cikin gidan akwai wurin wanka da kuma shakatawa. Bayan nan kuma akwai dakin motsa jini domin manyan ‘Yan wasa masu buga kwallon kafa.

Kwanaki ba da dadewa ba labari ya zo mana cewa tsohon Kocin na Real Madrid da babban ‘Dan kwallon na kasar Turai. Koci Zinedine Zidane za su hade da Cristiano Ronaldo a Juventus inda ya taba taka leda kafin zuwan sa Madrid.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng