Yadda Fayemi ya dawo ya zama Gwamna bayan ya sha kashi a 2014

Yadda Fayemi ya dawo ya zama Gwamna bayan ya sha kashi a 2014

Kun san cewa Kayode Fayemi ya lashe zaben Gwamnan Jihar Ekiti don haka ne mu ka kawo maku abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon Gwamnan.

Yadda Fayemi ya dawo ya zama Gwamna bayan ya sha kashi a 2014

Ministan Buhari Fayemi ya lashe zaben Gwamnan Ekiti

1. An haifi John Kayode Fayemi a shekarar 1965a Garin Isan-Ekiti da ke cikin Jihar Ekiti a yanzu. Sabon Gwamnan yayi karatun sa ne kan harkar tarihi da ilmin siyasa da na kasar waje a Legas da kuma Birnin Landan.

2. Bayan yayi karatu Kayode Fayemi yayi aiki da Hukumomin kasashen waje irin su ECOWAS, UN a matsayi da dama, Fayemi kuma yayi koyarwa a matsayin Malamin Makaranta. Sabon Gwamnan ya kuma yi rubuce rubuce da-dama.

KU KARANTA: An koka da yadda aka baza Jami’an tsaro wajen zaben Jihar Ekiti

3. A lokacin mulkin Soji a Najeriya, Fayemi yana cikin wadanda su ka fitini Gwamnati da adawa. Fayemi ne su ka kafa Rediyo Kudirat a wancan lokaci na mulkin Janar Sani Abacha yayin da su ke labe a Kasashen waje.

4. A 2010 ne Kayode Fayemi ya zama Gwamna bayan yayi fiye da shekaru 3 yana fama a Kotu. Kotu ta tsige Segun Oni daga Gwamna ta nada shi. Sai dai a 2014, shi ma ya sha kasa wajen Ayodele Fayose na PDP.

5. Bayan Fayemi ya sha kashi a zaben Gwamna ne ya gudanar da zaben fitar da gwanin takarar Shugaban kasa a APC da Buhari yayi nasara. Bayan nan ne aka nada Fayemi Minista. A bana ya ajiye aikin sa, ya tafi neman Gwamna karo na biyu.

Tsohon Ministan Ma’adanai na kasar Dr. Kayode Fayemi ya doke ‘Dan takarar PDP Farfesa Olusola Eleka a zaben sabon Gwamnan Jihar Ekiti da aka yi jiya. Abokin gaban sa na siyasa, Fayose ya sha kashi har a Karamar Hukumar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel