Yanzu Yanzu: Yan majalisar Imo sun fara tsare-tsaren tsige mataimakin gwamna Madumere
Majalisar dokokin jihar Imo, a ranar Talata, 10 ga watan Yuli sun fara tsare-tsaren tsige mataimakin gwamnan jihar, Eze Madumere, yayinda tashin hankalin siyasa ya ci gaba tsakaninsa da Rochas Okorocha.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ugonna Ozuruigbo ne ya tayar da batun tsige Madumere.
Ozuruigbo ya zargi mataimakin gwamnan da yin watsi da aikinsa da kuma matsayinsa na mutum na biyu a jihar na tsawon wasu lokuta.
KU KARANTA KUMA: Allah ya rigada ya kadarta cewa Buhari zai fadi a zaben 2019 - Galadima
Rahoton ya kara da cewa an mamaye majalisar wacce ke cike da tashin hankali da jami’an tsaro a fadin harabar majalisar dokokin.
An zargi Madumere da take doka.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng