Nigerian news All categories All tags
Wata mata mai ciki ta sha da kyar daga hannun masu satar mutane

Wata mata mai ciki ta sha da kyar daga hannun masu satar mutane

'Yan sandan jihar Kebbi sun ceci wata mata mai juna biyu, Hajiya Sadiya Tsoho, daga wata maboyar masu garkuwa da mutane a jihar

Wata mata mai ciki ta sha da kyar daga hannun masu satar mutane

Wata mata mai ciki ta sha da kyar daga hannun masu satar mutane

'Yan sandan jihar Kebbi sun ceci wata mata mai juna biyu, Hajiya Sadiya Tsoho, daga wata maboyar masu garkuwa da mutane a jihar.

Mai magana da yawun hukumar, DSP Mustapha Suleiman, ya tabbatar da hakan a ranar Lahadin nan data gabata, yace 'yan sandan sun samu nasarar ceto matar kuma babu kudin da 'yan ta'addar suka karba.

DUBA WANNAN: 2019: Kabilar Igbo sunce baza su zabi Atiku ba

Hajiya Sadiya, matar malam Anas Sha'aban, wanda yake da katon shagon sayar da kayan nan mai suna 'Sha'aban Supermarket' dake birnin Kebbi, ta bace ne a ranar Lahadin satin daya gabata, inda yan bindiga dadi suka je har gida suka sace ta, suka bi hanyar kauyen Mahuta dake kudancin jihar ta Kebbi da ita.

An ruwaito cewa, yan bindiga dadin sun ta jiran mijin ta a Rafin Atiku, dake Birnin Kebbi na tsawon awanni a ranar Lahadin, amma da basu ganshi ba kamar yanda suke tsammani, sai suka yanke shawarar bin shi gida.

Basu tarar dashi ba, sai matar shi mai dauke da juna biyu sukayi gaba da ita.

Daga baya suka kira mijin ta a waya tare da bukatar Naira miliyan 200 domin su sake ta.

Suleiman yace yan sandan su ceto matar a Mahuta, daga wurin wadanda suka sace ta, kara da cewa, bayan ta hadu da iyalanta, ana cigaba da bincike domin kama wadanda suke da hannu a lamarin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel