Gwamnan APC zai fice daga jam’iyyar saboda fin karfi da tsohon gwamna kuma sanata mai ci ke nuna masa
Alamu masu karfi daga Benuwe na nuni da cewar gwamnan jihar, Samuel Ortom, na shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar nan bada dadewa ba.
Wata majiya mai tushe ta shaidawa jaridar Nigeria Today cewar, shawarar gwamnan ta ficewa daga jam’iyyar ba zata rasa nasaba da shirye-shiryen hana shi tikitin kara tsayawa takara a jam’iyyar APC din ba a zaben 2019.
Majiyar ta bayyana cewar, gwamnatin tarayya ba ta gamsu da kokarin gwamna Ortom ba ta fuskar kawo karshen rikicin manoma da makiyaya da jihar ke fama da shi ba.
Tsohon gwamnan jihar, Sanata George Akume, ne mutumin da gwamnatin tarayya ta saka a gaba domin ganin an maye gurbin gwamna Ortom da wani dan takarar, kuma tuni har shirye-shirye sun yi nisa domin tsayar da wani tsohon dan majalisar wakilai, Mista Emmanuel Jime, da jam’iyyar ta APC ta hana tikitin takara a zaben shekarar 2015.
Fastoci da rigunan takarar Jime ne suka cika sansanin wakilan APC daga jihar Benuwe yayin zaben shugabannin jam’iyyar da aka gudanar kwanakin baya-bayan nan a Abuja.
DUBA WANNAN: Dalilin da yasa nake sukar shugaba Buhari – Sheikh Gumi
Tsohon gwamna Akume ne mutumin da ya taimaki Ortom ya zama gwamna a zaben 2015 kuma har yanzu shine ke rike da shugabancin jam’iyyar daga mazabu har matakin jihar ta Benuwe.
Tuni dai Ortom ya shaidawa ‘yan kwamitin yakin neman zabensa da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin dama sune mutanen day a so su karbi shugabancin jam’iyyar APC a jihar amma hakan bata yiwuwa ba.
Majiyar ta kara da cewar, abun da ya hana Ortom fita daga jam’iyyar shine rashin sanin inda alkiblar APC ya dosa.
Saidai, da aka tambayi sakataren gwamna Ortom na watsa labarai, Terver Akase, ya musanta rahoton cewar maigidan nasa na shirin fita daga jam’iyyar APC.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng