Kalli Idris Ahmed Kareko dan shekara 24 da ya daukaka martabar Najeriya yayinda ya kammala da sakamako mafi kyau a kasar China
Masu kwazo na cigaba da rusa shamakin da ke tsakanin bakake fata da farare. Akwa labarin matasa yan Najeriya maza da mata dake tabbatar da faruwan haka.
Wadannan maza da mata yan Najeriya na cigaba da daukaka martabar kasar ta hanyar yin iya bakin kokarinsu wajen ganin sun zamo kan gaba a fadin duniya.
Wani matashin dan Najeriya ya bi wannan sahu na daukaka martaban Najeriya bayan ya kammala da sakamako mafi kyawu daga wata babban jami’a a kasar Sin.
Ya zamo zakaran gwajin dafi da sakamako mafi inganci a fannin kimiyar kwamfuta dagfa jami’ar kimiya na Shenyang wato Shenyang University of Technology.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya fara rabon kudaden sata - Fashola
Legit.ng ta ci karo da labarin ne a shafin wani mai amfani da kafar sada zumunta na Facebook; wato Amtai Abdullahi Ali.
An bayyana sunan matashin mai shekaru 24 a matayin Idris Ahmed Kareka wadda ya fito daga yankin arewacin Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng