Nigerian news All categories All tags
Wata matashiyar budurwa ta hada baki da mahifiyarta ta kashe mahaifinta

Wata matashiyar budurwa ta hada baki da mahifiyarta ta kashe mahaifinta

A yau, Litinin, wata babbar kotun Abuja ta bayar da umarnin tsare wata matashiyar budurwa a gidan yari na garin Suleja bisa laifin hada baki da mahaifiyarta ta kashe mahaifinta.

Mai shari'a, Idris Kutigi, ya bayar da umarnin tsare uwar da diyarta a gidan yari ne bayan sun ki amsa tuhumar da ake yi masu na zargin kashe Mista Kusha Kure.

Kutigi ya daga sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Satumba.

Wata matashiyar budurwa ta hada baki da mahifiyarta ta kashe mahaifinta

Wata matashiyar budurwa ta hada baki da mahifiyarta ta kashe mahaifinta

Dan sanda mai gabatar da kara, Mista Fidelis Ogbobe, ya shaidawa kotu cewar wadanda ake zargin sun aikata laifin ne ranar 10 ga watan Maris.

Ya bayyana cewar, uwar da diyar dake sana'ar sayar da itace sun makure Mista Kure har saida ya mutu a gidansu dake kauyen Karavan a karamar hukumar Bwari ta Abuja.

DUBA WANNAN: An samu gawar mutane 10 rataye a wani gida, ana binciken musababbin mutuwar su

Dan sanda Ogbobe ya kara da cewar, diyar ce ta hallaka mahaifin nata saboda baya goyon bayan soyayyarta da saurayinta mai shekaru 24.

Kisa ne hukuncin kashe mutum a karkashin sashe na 221 na kundin tsarin fenal kod.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel