Kotu tayi umarnin garkame wani bature da ya auri ‘yar Najeria amma ya kashe ta tare da diyar da suka haifa

Kotu tayi umarnin garkame wani bature da ya auri ‘yar Najeria amma ya kashe ta tare da diyar da suka haifa

Peter Nelsen, baturen kasar Denmark, da ake zargi da kisan matar sa ‘yar Najeriya da diyar da suka Haifa ya samu matsuguni a gidan yari har zuwa watan Oktoba da za a fara sauraron karar sa.

A yau ne wata babbar kotu dake zaman ta a jihar Legas ta bayar da wannan umarni bayan gurfanar da Nielsen a gaban ta, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.

An gurfanar da Nielsen gaban mai shari’a, Bola Okikiolu-Ighile, bisa caji guda biyu da suka hada da kisan kai, laifin day a saba da sashe na 223 na kundin aikata manyan laifuka a jihar Legas.

Kotu tayi umarnin garkame wani bature da ya auri ‘yar Najeria amma ya kashe ta tare da diyar da suka haifa
Baturen da ake zargi da kashe matar sa 'yar Najeriya

Da yake shaidawa kotun laifin Nielsen, mai gabatar da kara kuma kwamishinan shari’a na jihar Legas, Adeniji Kazeem, ya ce Baturen mai shekaru 53, ya kasha matar sa, Zainab, mawakiya da kuma diyar da suka Haifa, Petra; mai shekaru uku a ranar 5 ga watan Afrilu a gidan su dake rukunin gidajen Banana Island a unguwar Ikoyi a Legas.

DUBA WANNAN: Mun daure Nyame da Dariye – EFCC ta fadi wani tsohon gwamna da zata mayar da hankali kan sa

Saidai, Nielsen ya musanta aikata laifuka da ake tuhumar sa da su. Lamarin da ya saka kotun umarnin a tsare shi a gidan yari tare das aka ranar da za,a fara sauraron shari’ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng