Idon wasu Samari biyu ya raina fata a gaban Kuliya bayan da suka kai ma wani hari da Adda

Idon wasu Samari biyu ya raina fata a gaban Kuliya bayan da suka kai ma wani hari da Adda

- Zafin kai ya kwashi wasu Samari sun tafka tsiya, sai dai sun yi luguf da suka bayyana gaban Kotu

- Matasan sun sassari abokin hayaniyarsu ne sannan suka sace wasu kayan amfani

An gurfanar da wasu Samari biyu gaban Alkali yau Litinin sakamkon farmaki da suka kaiwa wani Mutum da Adda har ta kai ga ya ji rauni bayan da wata hatsaniya ta ɓarke tsakaninsu.

Matasan biyun da aka gurfanar gaban wata Kotun Majistire dake zamanta a Ikeja sune; Kehinde Azeez da Ariyo Kazeem masu shekaru 21 da kuma 22, kuma ana zargisu da laifuka hadin baki don cuta da Sata da ɓarnata kaya da kuma yin duka ga wanda suke rikici.

Idon wasu Samari biyu ya raina fata a gaban Kuliya bayan da suka kai ma wani hari da Adda
Idon wasu Samari biyu ya raina fata a gaban Kuliya bayan da suka kai ma wani hari da Adda

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara Sajan Oshola Samuel, ya shaidawa Kotun cewa waɗanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 8 ga wata Afrilu a Unguwar Aboru ta jihar Legas.

Ya cigaba da shaidawa Kotun cewa, bayan ɓarkewar hayaniya tsakaninsu da Joseph Ochonu shi ne suka zaro Adduna wadda su kayi amfani da su wajen saransa, hakan ya sanya yaji raunuka a jikinsa.

Wannan ne ya basu damar sace wayar salula da kudinta ya kai Naira 47,000 da wsu batiran Mota biyu duk mallakar Ochonu sannan, suka fasa Gilashin gaban wata Mota mallakar wani mai suna Samuel.

KU KARANTA: 'Barayin Mai sun shiga Uku domin zamu toshe musu duk wata kofar numfashi – Sojojin Ruwa

Wannan laifuka dai sun saba da sashi na 173 da 287 da kuma 411 na kundin manyan laifuka na jihar ta Legas na shekara ta 2015.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa sashi na 172 ya tanadi hukuncin daurin shekaru uku yayinda sashi na 411 ya tanadi hukuncin shekaru biyu a gidan yari mutukar an same su da laifi.

Sai dai kuma bayan karanto musu laifukan nasu Matasan sun ki amsawa.

A don haka ne mai shari'a Mrs A. I. Abina ta bayar da belinsu ka kudi Naira N100, 000 kowannensu tare da kuma kawo wanda zai tsaya musu dake da shaidar biyan haraji ga Gwamnatin jihar Legas na shakaru biyu.

Snann ta dage shari'ar zuwa ranar 13 ga watan Yuli domin cigaban da sauraren karar. Kamar yadda NAN ya rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel