Ba surutu mu ke so ba, kudi wutan lantarki aka tambaye ka – BMO ga Obasanjo

Ba surutu mu ke so ba, kudi wutan lantarki aka tambaye ka – BMO ga Obasanjo

- An fadawa Shugaba Obasanjo ya ajiye cacar baki ya fito da wutan lantarki

- Kungiyar Buhari Media Organization tace ‘Yan Najeriya ba sakarkaru bane

- Shugaba Buhari ya caccaki tsohon Shugaban kasar na batar da kudi a banza

Mun samu labari cewa wata Kungiya ta Buhari Media Organization (BMO) ta fadawa tsohon Shugaban Kasar nan Cif Olusegun Obasanjo ya daina wani surutu ya fito da wutan Najeriya kurum.

Ba surutu mu ke so ba, kudi wutan lantarki aka tambaye ka – BMO ga Obasanjo
An taso Obasanjo a gaba kan batun wutan lantarki

Kungiyar ta BMO wanda ke bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta nemi Obasanjo ya ajiye batun zage-zage da cin mutunci da kiran mutane da wasu sunaye tare da yin dan waken zagaye kawai ya bayyana inda ya kai kudin wuta.

Buhari Media Organization tace tsohon Shugaban Kasar yayi ta wasu dogayen surutu ne amma har yanzu bai bayyanawa Jama’a inda ya kai Dala Biliyan 16 da ya kashe kan harkar wutan lantarki ba a lokacin yana mulkin kasar daga 1999 zuwa 2007.

KU KARANTA: Jihohi 24 da Gwamnatin Buhari ta ke rabawa ‘Yan Firamare abinci kyauta

Kungiyar da ke kare Shugaba Buhari tace ‘Yan Najeriya fa ba sakarkaru bane don haka akwai bukatar Cif Obasanjo yayi wa mutane lissafin yadda aka batar da wancan makudan kudi da kuma karuwar wutan lantarki da aka samu a Najeriya a lokacin.

Kungiyar ta nemi tsohon Shugaban Kasar Obasanjo ya ajiye wasu dabaru da yake yi ya fadawa mutane inda wutan lantarkin Najeriya ya shige bayan kashe Dalolin Amurka. Obasanjo dai ya nemi a karanta littafin sa a ji bayani lokacin da aka tado maganar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel