Mazan jiya: Ku sadu da Mista Taiwo Akinkunmi, mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya

Mazan jiya: Ku sadu da Mista Taiwo Akinkunmi, mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya

Tabbas tarihin Najeriya baya kammaluwa ba tare da an fadi sunan dattijon arzikin nan ba da ya yi anfani da bsiyar sa ya dauki tsawon lokaci sannan ya kirkiro tutar Najeriya da yanzu haka ake anfani da ita.

Tarihi dai ya nuna cewa tutar ta Najeriya dai wani bawan Allah ne mai suna Mista Michael Taiwo Akinkunmi da ke da shekaru 23 kacal a wancan lokacin ya kirkire ta a shekarar 1958 kafin daga bisani a amince da ita sannan a kaddamar da ita a ranar 1 ga watan Oktoba shekara ta 1960.

Mazan jiya: Ku sadu da Mista Taiwo Akinkunmi, mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya
Mazan jiya: Ku sadu da Mista Taiwo Akinkunmi, mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya

KU KARANTA: Wani babban malami ya lekowa Buhari faduwa a 2019

Legit.ng ta samu cewa sai dai kawo yanzu a iya cewa babu abun da ya canja a cikin tutar sai dai wani dan hoton jar tauraruwa dake a tsakiyar ratsin farin.

Turtar Najeriyar dai da ke dauke da kaloli biyu na kore da kuma ratsin fari na nuni ne da irin albarkar kasar noman Najeriya din da kuma zaman lafiyar ta.

Yanzu dai Mista Michael Taiwo Akinkunmi yana da akalla shekaru 82 a duniya kuma an kukan cewa gwamnatin kasar ta yi watsi da shi duk kuwa da irin gudummuwar da ya bayar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng