Sanatan Jam’iyyar APC ya soki masu rike da madafan iko a Najeriya

Sanatan Jam’iyyar APC ya soki masu rike da madafan iko a Najeriya

Mun samu labari cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya caccaki Shugaban kasa da Majalisar Tarayya da ma Jam’iyyun siyasa da keta mutuncin tsarin damukaradiyya ana Najeriya.

Sanatan Jam’iyyar APC ya soki masu rike da madafan iko a Najeriya
Sanatan Kaduna yace ana take dokokin kasa a Najeriya

Sanata Shehu Sani yace masu rike da madafin iko na yi wa dokokin kotu karan-tsaye yadda su ka ga dama a Kasar. Sanatan yace ba a bar Sojoji da ‘Yan Sanda da sauran Jami’an tsaro da sabawa dokar Kasar da su ka rantse za su kare ba.

KU KARANTA: Jam'iyyar SDP za ta fitar da 'Dan takara daga Arewa a 2019

‘Dan Majalisar na Jam’iyyar APC yayi anfani da shafin sa na Tuwita kamar yadda ya saba yace har da Gwamnonin Kasar cikin masu keta alfaramar tsarin farar hula. Sanatan yace hakan dai ba karamar barazana bace ga tsarin mulki.

Kwamared Shehu Sani wanda ya saba tofa bakin sa game da batutuwan da su ka shafi kasar tun kafin ya tafi Majalisar Dattawa ya koka da yadda Kotu ke bada umarni amma masu rike da madafan iko su yi mursisi su taka don son rai.

Sanatan na Kaduna yace yi wa tsarin ya zama kunun kanwar da duk masu mulki ke damawa a Najeriya. Ana zargin wannan Gwamnati dai da sabawa dokokin kotu ba sau daya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel