Ba kanta: Ana rigimar kan iyaka tsakanin jahohin Sokoto da Zamfara
Mataimakan gwamnonin jahohin Zamfara da kuma Sokoto dukan su da ke a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya kuma masu makwaftaka da juna sun jagoranci gudanar da wani muhimmin taro da nufin warware takaddamar kan iyakar su.
Taron dai wanda ya gudana a garin Sokoto ya samu halartar jami'an gwamnatocin jahohin da ma kuma hukumar kula da kan iyakoki ta gwamnatin tarayya.
KU KARANTA: Kotu ta sake kwace kudaden Patience Jonathan
Legit.ng haka zalika ta samu cewa mahalarta taron shawarci al'ummomin yankunan da ake takaddamar kan su da su kai zuciya nesa tare da rungumar zaman lafiya tsakanin su.
A wani labarin kuma, Akalla jam'iyyu 17 ne masu cikakkiya rijista da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa suka sanar da shirin su na yin hadin gwuiwa domin tunkarar zaben shekarar 2019.
Haka ma kuma gamayyar jam'iyyun sun ayyana shan alwashin su na fitar da dan takarar shugabancin kasa kwaya daya tilo da zai fuskanci shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin zaben.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng