Babu masaka tsinke: An yi taron murnar kara tsayawar Buhari takara a jihar Jigawa
- Magoya bayan jam´iyar APC a jihar Jigawa sun gudanar da taron gangamin nuna goyon bayan shugaba Buhari da gwamna Badaru Abubakar
- An gudanar da taron a filin kwallo na karamar hukumar Gumel kuma ya samu halattar kusan duk wani mai ruwa da tsaki dake jam´iyar APC a jihar
- Wani matashin dan siyasa, Mahadi Aminu Taura, ya ce shugaba Buhari da gwamna Badaru tamkar sun ci zaben 2019 sun gama
Magoya bayan jam´iyar APC a jihar Jigawa sun gudanar da taron gangami domin nuna goyon bayansu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a zaben shekarar 2019 mai zuwa.
Taron wanda akayi a filin kwallo na karamar hukumar Gumel ya samu halattar kusan duk wani mai ruwa da tsaki dake jam´iyar APC tare da sauran mambobin ta a jihar.
DUBA WANNAN: Mawakin da ya yi wakar cin zarafin Allah da manzon sa a Kano ya shiga hannu
Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki sun hada da Alhaji Isa Muhammad Gerawa wanda ya kasance shine shugaban kwamitin gudanar da taron, tsohon senator mai wakiltar jigawa ta gabas maso yamma, Sanata Danladi Sankara, da sanatan yankin mai ci a yanzu, da shugaban jam´iyyar Alhaji Ado Sani Kiri, 'yan majalisar tarayya da na jiha, da yan majalisar zartarwa na jiha, da kuma shugabannin kananan hukumomi da sauransu.
Wani matashin dan siyasa, Mahadi Aminu Taura, da ya halarci taron, ya shaidawa wakilin naij.con cewar, shugaba Buhari da gwamna Badaru tamkar sun ci zaben 2019 sun gama saboda irin kwazon da kishin son cigaban kasa da al'umma da suka nuna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng