Kalli hotunan yadda wata Amarya da mahaifinta ke bankwana cikin hawaye
Babu shakka soyayyar dake tsakanin ‘da da mahaifi wani sirri ne daga Allah. Sannan kuma rabuwa a tsakanin wadannan mutane biyu abu ne mai wahala.
Burin ko wani uba shine ya ga yarsa ta samu mijin aure a lokacin da ta isa yin aure.
Wadannan wasu hotunan Amarya ne da mahaifinta suke bankwana cikin hawaye lokacin da ake shirin tafiya da ita gidan mijinta.
Sauran 'yan uwa ma dake gurin saida suka zubar da hawaye, domin tausayawa shakuwar dake tsakaninsu.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya muka kama ‘Yan Shi’a 115 cikin masu zanga-zanga - ‘Yan Sanda
Kamar yadda wanda ya dauki hotunan, wato shahararren mai daukar hoton nan, Sani MaiKatanga ya bayyana, yace shima saura kadan ya zubar da hawaye saboda tausayawa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng