Jerin mutanen da su ka fi kowa yawan masoya a bana
Wannan karo kuma mun kawo maku jerin sanannun mutanen da ke da masoya ne rututu a Duniya kamar yadda alkaluma da hasashe su ka nuna a wannan shekarar ta 2018. Irin su Donald Trump sun samu kan su ne a wajen wannan jeri.
Ga jerin nan kamar yadda YouGov tayi bincike kwanakin baya sai dai babu ‘dan Afrika ko nutum guda:
1. Bill Gates
A nazarin da aka yi an gano cewa babu wanda aka fi kauna a Duniya yanzu haka irin Attajirin Duniyan watau Bill Gates na kasar Amurka.
2. Barrack Obama
Bayan Mai kudin Duniyan kuma wanda ya fi kowa farin-jini a Duniya shi ne tsohon Shugaban kasar Amurka Barrack Obama.
3. Jackie Chan
Chan na kasar China wanda yake fina-finai shi ne ya zo na 3 a Duniya a jerin da aka fitar. Jackie Chan yayi suna a Duniya baki daya.
KU KARANTA: Fina-finan Indiya da su ka fi kasuwa a bana
4. Xi Jinping
Jinping ne ya zo na 4 a jerin wanda shi ne Shugaban kasar China kuma Shugaban Rundunar Sojin kasar da Jam’iyyar kasar mai mulki.
5. Jack Ma
Jack Ma ‘Dan kasuwa ne wanda yayi fice da kamfanin sa na Ali Baba. Ma yana cikin wadanda su ka fi kowa karbuwa wajen jama’a.
6. Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha watau Vladimir Putin ne mutum na 6 a Duniya da ya fi kowa farin jini kamar yadda YouGov ta bayyana kwanan nan.
7. Dalai Lama
Dalai Lamai wanda ke kan kujera a yanzu yana cikin wadanda aka fi kauna a Duniya. Lamai shi ne Shugaban ‘Yan addinin Buda a Duniya.
8. Narendra Modi
Modi shi ne Firayim Ministan kasar India kuma kuma rikakken ‘Dan siyasa ne da ake ji da shi, yana cikin masu farin jinin Duniya a 2018.
9. Amitabh Bachchan
Tsohon Tauraron kasar Indiyan nan watau Amitabh ne ya zo na 9 a jerin. Mista Bachchan sananne ne kuma ya taba yunkurin shiga siyasa.
10. Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo ne ya rufe jerin inda ya zama ‘Dan wasan kuma kurum da ya shiga cikin sahun wadanda aka fi nunawa kauna a Duniya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng