Masu mota sun yabama Dangote kan aikin titin Obajana-Kabba
Masu mota da matafiya daga arewa zuwa Kudu da kuma kudu zuwa arewa, sun yabama gidauniya Dangote bisa ingantaccen aikin da yayi a hanyar Obana-Kabba wanda ya zamo shimfidadden titi mafi tsawo a kasar.
Sashin masu motan wanda sukayi Magana a karshen mako sun bayyana cewa aikin titin ya fara taimakawa tare da saukaka tafiye-tafiye a fadin yankunan.
Wani dan kasuwa daga Arewa, Abubakar Umar wanda ya yabama shugaban gidauniyar ta Dangote, Aliko Dangote ya bayyana aikin a matsayin babban kwanciyar hankali domin tuni ya fara saukaka tafiye-tafiye da kuma hadi a fadin yankunan.
A nasa bangaren, wani mashawarci, Mista Abdullahi A. Umar wanda kanyi tafiya daga Okene a jihar Kogi yace shi a yanzu hanyar Obana-Kabba yake bi sannan kuma yayi kira ga sauran kamfanoni da suyi koyi da Dangote.
Wasu daga cikin masu motoci da suka tofa albarkacin bakunansu sun bukaci gwamnati a dukkan matakai dasu hada hannu da gidauniyan Dangote wajen aikin hanyoyi.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Ribas ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya ke nufin sa da sharri
A halin da ake ciki, manajan darakta na kamfanin da sukayi aikin titin Dandote, Mista Ashif Juma ya bayyana cewa zaa kammala aikin hanyan na Obajana-Kabba zuwa watan Disamba na wannan shekaran kamar yadda aka shirya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng