Tinubu ya bayar da sunayen 'yan takara 5 da zasu maye kujerar shugaban jam'iyyar APC

Tinubu ya bayar da sunayen 'yan takara 5 da zasu maye kujerar shugaban jam'iyyar APC

A yayin da ake ta samun rafkanuwa da rikice-rikicen jayayya a tsakanin shugabanni da gwamnonin jam'iyyar APC, NAIJ da sanadin jaridar Daily Trust cikin zakule-zakulen ta ta kawo muku jerin sunayen 'yan takara biyar da zasu maye gurbin kujerar shugabancin jam'iyyar kamar yadda tsohon gwamnan jihar Legas Asiwaju Bola Tinubu ya fitar.

Rahotannin sun bayyana cewa, a ranar Talata da ta gabata shugabanni da gwamnonin jam'iyyar suka gudanar da taro tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa ta Villa, inda ta Legit.ng ta ruwiato cewa taron ya watse baram-baram sakamakon banbancin ra'ayoyi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kimanin gwamnoni 20 na jam'iyyar sun bayyana ra'ayin su na rashin amincewa da tsawaita wa'adin shugaban jam'iyyar akan kujerar sa a madadin gabatar da zaben shugabannin jam'iyyar a gangamin ta da ake sa ran gudanar wa a watan Yuni.

Tinubu ya bayar da sunayen 'yan takara 5 da zasu maye kujerar shugaban jam'iyyar APC

Tinubu ya bayar da sunayen 'yan takara 5 da zasu maye kujerar shugaban jam'iyyar APC

A sakamakon haka Legit.ng da sanadin jaridar Daily Trust ta kawo muku jerin sunayen 'yan takata biyar da Tinubu ya bayar da za su maye gurbin kujerar shugaban jam'iyyar Cif John Odigie-Oyegun.

KARANTA KUMA: Gwamnonin APC 2 na neman kiran taron shugabannin jam'iyya da ya sabawa ka'ida

Jerin 'yan takara da Tinubu ya bayar da sunayen su sun hadar da; Sanata Abu Ibrahim da Sanata Lawal Shu'aibu daga yankin Arewa maso Gabas, Alhaji Kashim Imam da tsohon Sakatare gwamnatin tarayya Babachir David Lawal daga yankin Arewa maso Gabas, sai kuma Sanata George Akume na yankin Arewa ta Tsakiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel