Dalilin da yasa muka caccaki Buhari a babban masallacin tarayya – Yan Shi’a

Dalilin da yasa muka caccaki Buhari a babban masallacin tarayya – Yan Shi’a

Yan kungiyar IMN da aka fi sani da yan Shi’a sun tabbatar da cewa lallai mambobinsu ne suka caccaki shugaba Muhammadu Buhari ranan Juma’an da ya gabata a babban masallacin tarayya, Abuja.

Kafafen yada labarai sun bada rahoton cewa wasu mabiya Shi’a sun yi zanga-zanga a masallacin Juma’a inda shugaba Buhari ya zo Sallah amma fadar shugaban kasa ta musanta hakan.

Dalilin da yasa muka zazzagi Buhari a babban masallacin tarayya – Yan Shi’a
Dalilin da yasa muka zazzagi Buhari a babban masallacin tarayya – Yan Shi’a

Kungiyar ta ce mambobinta sun dau wannan mataki ne saboda shugaba Buhari ya ki sakin shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky bayan shekaru 2 yanzu.

KU KARANTA: Za’a gurfanar da Dino Melaye tare da yan bindiga 4 ranan 10 ga Mayu

A wani hira da mamban kungiyar Abdullahi Muhammad Musa ya gabatar, ya ce suna zanga-zangan lumana ne domin nuna zaluncin gwamnatin tarayya da cutan hukumar sojin Najeriya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng