Kungiyar Kiristocin Najeriya sun yi kashedi ga malaman addini dake wa'azi mai zafi

Kungiyar Kiristocin Najeriya sun yi kashedi ga malaman addini dake wa'azi mai zafi

Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya Dakta Samson Ayokunle tare da hadin gwuiwar wasu sauran masu ruwa da tsaki na kungiyar sun ayyana kashedin su ga malaman addinai a Najeriya da ma sauran masu fada aji akan yin wa'azuzzuka masu zafi da nufin tunzura jama'a.

Wannan kashedin dai na zuwa ne a ta bakin shugaban na kungiyar CAN yayin da yake jawabi a wajen taron shugabannin addinai a kasar nan da aka gudanar a ranar Alhamis din da ta gabata a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Kungiyar Kiristocin Najeriya sun yi kashedi ga malaman addini dake wa'azi mai zafi
Kungiyar Kiristocin Najeriya sun yi kashedi ga malaman addini dake wa'azi mai zafi

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari na ganawa da yan matan Dapchi

Legit.ng ta samu cewa Dakta Samson ya kuma kara da cewa hakika irin wa'azuzzukan nan da malaman addinai ke yi suna taka muhimmiyar rawa wajen tunzura mazauna kasar tare da kuma ruruta wutar rikicin addini da kuma wani lokacin kabilanci.

A wani labarin kuma, Wata kungiya da ta kira kanta ta jiga-jigan masu ruwa da tsaki da ma gudanarwar jam'iyyar APC ta yi kira ga shugabannin jam'iyyar a mataki na kasa da su hukunta dukkan wadanda suka kai jam'iyyar kotu ba tare da yin anfani da dukkan matakai na cikin gida ba game da batun karin wa'adin mulkin shugabannin ta.

Su dai wadanan 'yan kungiyar sun bayyana hakan ne biyo bayan wani zama na musamman da suka gudanar a garin Abuja inda kuma suka fitar da sanarwar bayan taro tare da bayyana matsayar su ga manema labarai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng