Rikicin Taraba: Mutane 29 sun rasa rayyukansu, an tsananta dokar hana fita

Rikicin Taraba: Mutane 29 sun rasa rayyukansu, an tsananta dokar hana fita

- An sake gano gawawakin al'umma da suka rasu sakamakon rikicin kabilanci da ya barke a wasu sassan tsibirin Mambilla

- Barkewan rikicin ya sa gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba ya saka dokar hana fita daga safe har dare

- Hukumar Yan sanda ta ce komi ya lafa a yankunan da rikicin ya barke

Gwamanatin jihar Taraba ta kafa dokar hana fita a garin Mayo Ndaga da ke karamar hukumar Sardauna bayan wani sabon rikici ya barke tsakanin matasan tsibirin Mambilla da matasan Fulani.

Garuruwan da aka saka dokar hana fitan sun hada da Mayo Ndaga, Yarimaru, Kakara, Sherif da kuma wasu garuruwa kan iyakan Najeriya da Kasar Kamaru kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito

Rikicin Taraba: Mutane 29 sun rasa rayyukansu, an tsanta dokar hana fita
Rikicin Taraba: Mutane 29 sun rasa rayyukansu, an tsanta dokar hana fita

Shugaban karamar hukumar Sardauna, Godwin Sol, ya bayyana cewa an gano gawawaki guda 29 a jiya kuma har yanzu ana cigaba da neman wasu.

KU KARANTA: EFCC ta sake gurfanar da tsohon sakataren INEC bisa laifin karbar cin hanci daga Diezani

Majiyar Legit.ng kuma ta ruwaito cewa gwamnan jihar na Taraba, Darius Ishaku ya kira wani taron gagawa tare da kwamishinan yan sandan jihar, David Akinremi, Shugaban Yan sandan farin kaya DSSS da sauran shugabanin hukumomin tsaro a jihar.

Mai bawa gwamnan shawara na musamman kan fannin sadarwa, Mista Bala Dan Abu ya tabbatar da taron da gwamnan ya kira amma bai bayyana abin da aka tattauna a taron ba.

Jami'in hulda da jama'a na Yan sanda Jihar, ASP David Misal bai amsa wayar sa sai dai ya aike ta sakon kar ta kwana ga jami'in Daily Nigerian inda ya shaida masa cewa "Komi ya lafa a yankunan"

Rikicin dai ya samo asali ne tun ranar Laraba na makon da ya wuce bayan wasu sun kai hari a garuruwan Fulani da ke Yarimaru kuma daga baya rikicin ya watsu zuwa wasu bangarorin tsibirin na Mambilla.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164