Banza ta fadi: Hukumar DPR ta rabar da litan mai 40,000 ga al’ummar jihar Kaduna

Banza ta fadi: Hukumar DPR ta rabar da litan mai 40,000 ga al’ummar jihar Kaduna

Hukumar kula da man fetir ta kasa, DPR ta rabar da man fetir da yawansa lita dubu arba’in (40,000) wanda aka karkatar da shi, a wani gidan mai na daban a jihar Kaduna.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hakan na daya daga cikin matakan da hukumar ta sha alwashin bi domin tabbatar da masu gidajen mai sun daina karkatar da man fetir, domin a shawo kan matsalar karancin man.

KU KARANTA: Kisan mutane 41 a Zamfara: Bamu tabbatar da kashe kashen ba, a Rediyo muka ji – Gwmanatin jihar Zamfara

Shugaban hukumar na reshen Arewa, Yahaya Maishera ya bayyana cewa wannan man da aka rabar kamata yayi a kai shi jihar Gombe ne, amma sai suka tsince motar dakon man a garin Funtua na jihar Katsina.

Banza ta fadi: Hukumar DPR ta rabar da litan mai 40,000 ga al’ummar jihar Kaduna
Gidan mai

Yahaya ya cigaba da fadin bincikensu ya nuna takardun daukan mai da motar ke dauke shin a bogi ne, saboda sun nuna an yi lodin man a ranar 6 ga watan Feburairu a garin Legas, sai ga shi kuma an kama su a hanyar Zamfara a ranar 9 ga wata, inda ya kara da cewa a yanzu suna bin sawun masu man da masu dakon man.

Daga karshe Yahaya yace sun kwace motar, kuma sun rabar da man ga masu ababen hawa a kayadajjen farashi a gidan man NNPC dake Mando na jihar Kaduna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng