Jam’iyyar APC ta saukaka mana hanyoyin cin zaben 2019 – Makarfi

Jam’iyyar APC ta saukaka mana hanyoyin cin zaben 2019 – Makarfi

- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, tsohon Sanata, kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na rikon kwarya, Ahmed Makarfi, ya ce jam’iyyar APC zata sha kaye a hannun PDP a zabukan 2019

- Makarfi ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da wakilin jaridar Vanguard a karshen satin day a wuce a jihar Legas

- Ya bayyana cewar shi yanzu mai bayar da shawara ne a cikin jam’iyyar PDP bayan gama wa’adin mulkinsa na rikon kwarya

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, tsohon Sanata, kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na rikon kwarya, Ahmed Makarfi, ya yi wata ganawa da wakilin jaridar Vanguard a karshen satin da ya wuce a jihar Legas inda ya yi tsokaci a kan batutuwa da suka shafi kasa da kuma harkokin siyasa, musamman batun zaben 2019 dake kara karatowa kullum.

Jam’iyyar APC ta saukaka mana hanyoyin cin zaben 2019 – Makarfi

Ahmed Makarfi

Da yake amsa tambaya a kan batun zaben shugabannin jam’iyyar PDP da ya gudana, Makarfi, ya bayyana cewar ya yi iya bakin kokarinsa wajen tabbatar da dimokradiyya a zaben shugabannin jam’iyyar, sannan ya kara da cewar, ba wani bakon abu bane bayan kammala zabe wadanda basu samu nasara ba su bijiro da korafe-korafe da koke-koke.

DUBA WANNAN: 2019: Hotunan taron bude ofishin takarar Sule Lamido a mahaifar sa

Ya kara da cewar tunda yanzu ba shine ke shugabancin jam’iyyar ba, ba zai iya sanin dukkan matakan da shugabancin jam’iyyar ke dauka ba domin sulhunta wadanda basu ji dadin yadda zabukan jam’iyyar suka gudana ba.

Da yake tsokaci a kan shirin jam’iyyar PDP dangane da zaben 2019, makarfi ya bayyana cewar “babu jam’iyyar dake da burin zama jam’iyyar adawa har abada, burin jam’iyyar adawa shine ta karbi mulki. Muna godiya ga jam’iyyar APC domin ta saukaka mana wahalar yakin neman zabe. Na tabbata ‘yan Najeriya basa bukatar ci gaba da shan wahala, a saboda haka za suyi abinda ya dace a shekarar 2019.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel