Shugaban hukumar 'Yan Sandan Najeriya ya nufi garin Zurmi da ke Jihar Zamfara domin magance matsalar tsaro
- A yau ne babban sufeton 'yan sanda zai je garin zurmi
- Matsalar tsaro na ta ta'azzara a kasar nan
A ranar Asabar dinnan ne Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya, Ibrahim Kpotun Idris, ya nufi garin Zurmi dake Jihar Zamfara domin shawo kan matsalar tsaro a yankin.
DUBA WANNAN: Wasika ga shugaba Buhari kan yaki da Boko Haram
A ranar Alhamis din da ta gabata ne wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, suka kai hari kauyen Birane dake cikin karamar hukumar Zurmi, a jihar Zamfara, inda suka kashe sama da mutune arba'in.
Shugaban hukumar 'yan sandan ya bar garin Lagos a yau Asabar dinnan 17 ga watan Febrairu 2018, ya nufi garin Katsina, inda daga nan zai nufi garin Zurmin dake jihar Zamfara.
Duk da yake ana ganin cewa ire-iren wadannan hare haren sun dan ragu a jihar ta Zamfara, lamarin na kokarin sake dawowa, domin a watan Nuwamba da ya gabata, an kai irin wannan hari a karamar hukumar Mulki ta Shinkafi, inda aka kashe mutane kusan ashirin da hudu tare da kona gidaje da dama.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng