Sharudda 10 da zaka cika wajen neman shiga aikin 'yan sanda

Sharudda 10 da zaka cika wajen neman shiga aikin 'yan sanda

Hukumar 'yan sanda ta Najeriya, tana gayyatar daukacin al'umma mabuƙata kuma da suka cancanta wajen daukan su aiki a matakin ƙaramin ma'aikaci wato kurtu, inda a turance ake cewa constable.

Jami'an 'yan sanda yayin gudanar da atisaye
Jami'an 'yan sanda yayin gudanar da atisaye

Jaridar The Nation da sanadin kakakin hukumar, CSP Jimoh Moshood, ya bayyana hakan a ranar talatar da ta gabata, inda ya bayar da sanarwar buƙatu tare da sharuɗɗa da ya kamata masu sha'awar shiga aikin su cika kafin a ɗauke su aikin.

Legit.ng ta kawo muku jerin sharuɗɗan da sanadin jaridar ta The Nation kamar haka:

1. Mabukaci ya kasance haifaffe kuma ɗan asalin kasar Najeriya tare da lambar katin ɗan ƙasa, sa'annan kada shekaru su wuce 18 zuwa 25.

2. Ka kasance ka yi nasara a darussa biyar na jarrabawar fita daga sakandire da suka haɗar da lissafi da kuma yaren turanci a zaman zana jarrabawar da bai wuce karo biyu ba.

3. Kasancewar mutum na gari mai kyawawan ɗabi'u da ba a taba kama sa da wani laifin ta'addanci ba.

4. Ana buƙatar tsayin maza kada ya yi ƙasa da mita 1.67 da kuma tsayin mata kada ya yi ƙasa mita 1.64.

5. Faɗin kirjin maza kada ya kasance ƙasa da inci 34.

6. Mutum ya kasance mai cikakkiyar lafiya ta kowane bangare a halittarsa.

7. Kada mata su kasance masu juna biyu a yayin gudanar da ɗaukar aikin.

8. Kada ya kasance ana bibiyar mutum bashi da ko kuma mai fama da kansa ta fuskar tattalin arziki.

9. Mabuƙata su tabbatar da samun takardu daga shafin hukumar na yanar gizo, ta shaidar amincewar iyayen su da kuma waɗanda zasu tsaya musu a matsayin jingina.

10. Sharaɗi na cikon ƙarshe shine, wajibi ne ga mabuƙata su tabbatar da an duba lafiyar su.

Hukumar 'yan sandan ta kuma gargaɗi mabuƙata akan cewa wannan harƙallar ta ɗaukan aiki kyauta ce, saboda haka su ankare da macuta da mayaudara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng