Masoya sun roki Kwankwaso ya hakura da takara a 2019 a wata budaddiyar wasika
- Magoya Sanata Rabiu M. Kwankaso sun nemi ya hakura da takara
- Masoyan tsohon Gwamnan sun ce ya dakatar da shirin zabe a 2019
- Watakila Kwankwaso ya nemi kujerar Shugaban kasa a APC badi
Mun ji cewa Masoya sun roki tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya hakura da neman takarar Shugaban kasa a zaben 2019. Wasikar ta wani Saurayi 'Dan kwankwasiyya Adnan Muktar Adam Tudun-Wada ta fito ne a Jaridar Daily Trust.
A makon nan ne mu ka ji cewa wasu daga cikin magoya bayan Sanatan na Kano ta tsakiya sun aika masa budaddiyar wasika inda su ka nemi ya janye maganar neman kujerar Shugaban kasa a zaben da za ayi shekara mai zuwa.
KU KARANTA: Matasan Daura sun tsaida Shugaba Buhari takara
A takardar an nemi Sanatan ya dakata har sai bayan Shugaban Kasa Buhari ya kammala wa’adin sa, sannan kuma watakila a mulkin kasar ya koma Yankin Yarbawa na tsawon shekaru 8 kamar yadda ake kama-kama a kasar.
Ana dai sa rai a karshen wannan watan, Sanatan zai kai ziyara Jihar Kano tare da magoya bayan sa. A zaben 2014 na fitar da gwani a APC, tsohon Gwamnan ne ya zo na biyu bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng