Yarima ne ya fi cancanta da mulkin Najeriya a 2019 - Kungiyar matasan Arewa

Yarima ne ya fi cancanta da mulkin Najeriya a 2019 - Kungiyar matasan Arewa

- Wata kungiyar matasan Arewa ta fito fili ta bayyana goyon bayanta ga Yarima

- Kungiyar ta bayyana Yarima a matsayin dan siyasa da halin kirki

- Sun ce zai dora a kan aiyukan shugaban Buhari

Wata kungiyar matasan Arewa (Northern Youth Assembly) ta fito fili ta bayyana goyon bayanta ga tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani (Yariman Bakura) a matsayin dan takarar shugabancin kasa a zaben shekarar 2019.

Yarima ne ya fi cancanta da mulkin Najeriya a 2019 - Kungiyar matasan Arewa
Ahmad Sani

A wata takarda da shugaban kungiyar da sakatarensa, Abdulrahman Tumbido da Saminu Muazu, suka raba ga manema labarai, sun ce sun yanke shawarar goyawa Yarima baya bayan zaman da shugabannin kungiyar suka gudanar a Abuja. Sun bayyana Yarima a matsayin dan siyasa mai halin kirki da zai kawowa Najeriya cigaba.

DUBA WANNA: Bamu da masaniyar ko Buhari zai tsaya takara a 2019 - APC

A cewar su, Najeriya na bukatar gwarzon namiji kamar Yarima, suna masu bayar da tabbacin cewar zai dora a kan dukkan aiyukan da shugaba Buhari ya fara.

Sanata Ahmad Sani tsohon gwamnan jihar Zamfara karo biyu, yanzu kuma Sanatan Najeriya, ya taba neman takarar shugabancin kasa a karkashin tsohuwar jam'iyyar ANPP. Saidai ya janye takarar sa tun kafin a gudanar da zaben fitar da dan takarar na cikin gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng