Abin da ka shuka: Za’a kashe mutanen da suka kashe ‘Baban’ ministan Buhari ta hanyar rataya
Hausawa kan ce ‘abin da ka shuka, shi zaka girba’ a jiya ne wata babbar kotun jihar Delta ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu gungun bata gari, wadanda suka kashe kawun ministan Buhari.
Mista Diokpa Felix Boise, wanda kanin mahaifi ne ga karamin ministan mai, Ibe Kachikwu ya gamu da ajalinsa ne a hannun wasu leburorinsa, dake yi masa aiki a gona, inda suka kashe shi a ranar 9 ga watan Yunin 2014.
KU KARANTA: Yaron Atiku yayi watsi da hukuncin Kotu, ya ƙwace Ɗansa daga hannun Uwarsa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito maharan da sunanan ya hada da :Sunday Luka, Danjuma Kaika da Luka Agu, dukkaninsu yan jihar Nassarawa sun kashe mutumin ne ba gaira babu dalili, sa’annan suka arce da motarsa kirar Kia Rio.
Bayan sauraron kararrakin da aka shigar dasu kan tuhutuhume guda 4, Mai shari’a C.I Ogisi yace babu makawa sai ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya, shi ne hukuncin daya dace da su.
Da alamu minista Ibe Kachikwu zai farin ciki da wannan hukuncin Kotu, musamman yadda yayi jimamin mutuwar kawun nasa mai shekaru 75 kafin rashin sa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng