Dubi yadda Buhari ya yi murnar zagayowar ranar haihuwar sa bayan yaki amincewa a yi masa fareti
- Yau, Lahadi 17 ga Disamba, shugaba Buhari ya cika shekara 75 a duniya
- Shugaban yaki amincewa da a yi masa faretin murnar zagayowar ranar haihuwar sa
- Daga shi sai na kusa da shi suka yi murnar su a fadar gwamnati
Fadar mulkin Najeriya, Aso Villa, ta saki hotunan shugaba Buhari a yayin da yake murnar zagayowar ranar haihuwar sa tare da makusantan sa.
Rahotanni sun bayyana cewar tun farko shugaban kasar yaki amincewa da ayi masa faretin murnar cika shekaru 75. Buhari ya zabi yin shagalin murnar wannan rana da iyali da kuma makusantan sa kamar yadda kuke gani cikin hotunan da fadar shugaban kasar ta saki a kafar ta, ta watsa labarai.
DUBA WANNAN: Dubi jerin hanyoyi da gadoji da gwamnatin APC ta ce ta kammala cikin shekaru 2 kacal
Wata majiya a fadar shugaban kasar ta bayyana mana cewar duk da kin amincewa da taron shagalin biki domin wannan taya shi murnar zagayowar wannan rana, wasu jami'an gwamnati sai sun bi wasu hanyoyin domin gudanar da bikin wannan rana a madadin shugaban.
An haifi shugaba Buhari a ranar 17 ga watan Disamba, shekarar 1942, a garin Daura, dake jihar Katsina. Buhari ne da na 23 a wurin mahaifin su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng